Jam’iyyar PDP ta amincewa yankin arewa ya fitar da dan takarar shugaban kasa

0 105

Tsohon Gwamnan Jihar Niger Dr Babangida Aliyu ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta amincewa yankin arewa ya fitar da dan takarar gwamnan shugaban kasa daga yankin biyo bayan cimma yarjejeniya da sukayi.

Babangida ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a lokacin da kungiyyar magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abukar suka kai masa ziyara a gidansa dake Minna babban birnin jihar.

Ya kuma tabbatarwa kungiyyar cewa zata kai ga gaci, zai kuma goya musu baya.

Tsohon gwamnan ya kuma yabawa yan kungiyyar musamman yanda suke bi lungu da sakon kasar nan domin daga likafa da neman marawa Atiku Abubakar baya a 2023.

Anasa bangaren ko’odinatan kungiyyar na kasa Dr Victor Moses, ya godewa tsohon gwamnan bisa nuna sha’awarsa ta marawa Atiku Abubakar baya a zaben 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: