Sai Shugaba Buhari ya gyara wutar lantarkin Najeriya kafin ya sauka a 2023 – Garba Shehu

0 95

Babban mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu buhari malam Garba Shehu yace yanzu Nigeria ta samu nasarar samun wutar lantarki mai karfin megawatts dubu 13.

Ya bayyana hakan ne a lokacin dayake tattaunawa da manema labarai akan ayyukan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma birinsu na kammala ayyukan gwamnatin kafin karshen wa’adinsa da zai kare a 2023.

Ya kuma kara da cewa biyo bayan cece-kuce da akeyi cewa, gwamantin Shugaba Buhari bazata kammala ayyukanta ba, ya tabbatar da cewa zasu kammala kafin ya sauka.

Ya kuma fadawa yan kasarnan cewa dole ne su kasance masu hakuri musamman halin da yan kasar nan suka tsinci kansu a ciki a farkon wannan mulkin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: