Shugaban kasa Muhammadu a jiya juma’a a babban birnin tarayya Abuja ya bukaci sabbin shugabannin kamfanin mai na kasa NNPC da su kasance masu bin dokoki da ka’idojin hukumar tare daga likafar kamfanin, wajan nagarta,gaskiya da kuma adalci.

Yayin kaddamar da sabbin shugabannin shugaban kasar ya kuma bukace su, da su maida hankali akan samun riba da samarwa kasar nan kudade daga kasashen duniya.

Sabbin mutanen da aka kaddamar sun hada da Senator Okadigbo a matsayin shugaba, sai Mele Kolo Kyari da kuma Umar I. Ajiya.

Sauran sune Dr Tajudeen Umar, Mrs Lami O. Ahmed Mallam Mohammed Lawal, Engr. Henry Obih, Barrister Constance Harry Marsha, Chief Pius Akinyelure, Dr Nasir Sani Gwarzo da kuma babban daraktan ma’aikatar kudi ta kasa wanda aka nada Aliyu Ahmed.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: