Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamna Namadi ya nemi afuwarta kan yaga katin jam’iyyarta da yayi

0 705

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karbi wasu sabbin ‘yan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya nuna alamar kin amincewa da tsohuwar jam’iyyarsu ta hanyar yaga katin shaidarsu a sarari, lamarin daya sanyan yan adawar ke kira ga gwamnan ya fito ya bayyana nadamar sa a fili.

Gwamnan ya bayyana hakan ne da yammacin Litinin, yayin wani taron karbar sabbin mambobi a birnin Dutse da aka gudanar a fadar gwamnati.

A cewarsa, PDP ta riga ta rasa farin jini a jihar Jigawa, inda ya ce mafi yawan mambobinta sun riga sun fice zuwa jam’iyyar APC. Ya kara da cewa sabbin mambobin za su samu cikakken matsayi a cikin jam’iyyar, kuma za a yi musu adalci kamar tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar.

A madadin wadanda suka sauya shekar, Nasir Alhassan ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Namadi bisa irin tarba da karamcin da suka samu.

Ya ce mutum fiye da 500 ne suka fice daga PDP suka koma APC domin su taimaka wajen ci gaban jihar Jigawa.

Alhassan ya ce rashin jagoranci mai ma’ana da tabarbarewar tsari ne ya sa suka yanke shawarar ficewa daga PDP. Ya kara da cewa a halin yanzu, APC ce ke da rinjaye a jihar, inda ya danganta hakan da irin jajircewar da Gwamna Namadi ke nunawa da karbuwar da yake da ita a cikin al’umma.

Leave a Reply