Jihar Jigawa Ce Mafi Zaman Lafiya A Faɗin Najeriya

0 146

An bayyana jihar Jigawa a matsayin jihar data fi zaman lafiya a tsakanin jihohin ƙasar nan talatin da shida.

Kwamandan kwalejin horas da jami’an gidajen yari dake Kaduna, Alhaji Muhammad Ibrahim Hussaini ne ya tabbatar da haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa ofishin mataimakin gwamnan jiha Alhaji Umar Namadi.

Ya ce bisa bayanan da suka tattara sun lura cewa jihar Jigawa jiha ce data fi zaman lafiya da karancin aikata laifuka wanda hakan yasa ta cigaba ta fuskar tattalin arziki.

Alhaji Muhammad Hussaini ya ce yan tawagar sun gano cewa akwai ayyukan cigaba da dama da aka gudanar a yankunan kananan hukumomin da suka ziyarta domin yinkurin gwamnati na inganta harkokin noma.

Da yake maida jawabi mataimakin gwamnan Alhaji Umar Namadi ya ce gwamnati mai ci a yanzu ta maida hankali ne kan ayyukan inganta rayuwar Dan Adam a wani mataki na rage fatara da talauci.

Ya ce gwamnati tana yin dukkanin abinda ya dace wajen samar da hanyoyin bunkasa tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: