Jihar Kano tana da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi kimanin miliyan biyu, a cewar Buba Marwa

0 64

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Buba Marwa, ya fada jiya a Kano cewa jihar Kano tana da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi kimanin miliyan biyu, wato kashi 16 cikin dari na mutanen jihar.

Buba Marwa ya bayyana hakan lokacin da ya kai wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ziyarar ban girma.

Ya ce a jihar Kano, a cikin kowane mutum shida, daya mai shan muggan kwayoyi ne, kuma suna tsakanin shekaru 15 zuwa 64 a duniya.

Ya kara da cewa jihar Kano tana da masu amfani da miyagun kwayoyi kusan miliyan biyu da ke amfani da tramadol da codeine da sauran magungunan tari, maimakon tabar wiwi.

Shugaban ya yi bayanin cewa tun lokacin da ya zama shugaban hukumar a watan Janairun bana, hukumar ta kwace sama da kilo miliyan biyu na kwayoyi iri daban-daban, wanda aka kiyasta kudinsu ya kai biliyoyin Nairori.

Buba Marwa ya ce an kama mutane dubu 8 kuma dubu mutane 1 da 600 yanzu haka suna zaman kaso a gidajen gyaran da’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: