Akalla mutane 43 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar Borno

0 57

Akalla mutane 43 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar Borno. Ya zuwa yanzu an samu rahoton bullar cutar a jikin mutane 559.

Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Juliana Bitrus a hukumance ta bayyana barkewar cutar a wani taron manema labarai yau a Maiduguri.

Ta bayyana cewa karamar hukumar Gwoza ita ce karamar hukumar da cutar ta fi kamari, inda mutane 353 suka kamu da cutar sannan 18 suka mutu.

Karamar Hukumar Kaga akwai mutane 22 da suka harbu da cutar, tare da mutuwar mutane biyu. An samu mutane 126 da suka harbu da cutar a Hawul, inda mutane 11 suka mutu.

Akwai mutane 6 a Magemeri inda mutum daya ya mutu, sai Damboa mai mutane 39 da mutuwar mutane 10, mutane 10 sun harbu a Jere inda mutum guda ya mutu.

Kwamishiniyar ta yi kira ga jama’a da su guji duk wani abin da zai kara dagula lamarin, yayin da gwamnati ta dauki matakan tabbatar da shawo kan barkewar cutar cikin kankanin lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: