‘Yan bindiga sun fusata kan rufe kasuwannin mako-mako da gwamnatin jihar Zamfara ta yi

0 104

‘Yan bindiga da aka ce sun fusata kan rufe kasuwannin mako-mako da gwamnatin jihar Zamfara ta yi, sun kashe wani jami’in karamar hukuma da wata ‘yar kasuwa a jihar.

Wani injiniya kuma daraktan ayyuka a karamar hukumar Kauran Namoda mai suna Umaru Moriki, da wata shahararriyar ‘yar kasuwa a yankin mai suna Rumba Jengeru, an kashe su lokacin da ‘yan fashin dajin suka bude wa matafiya wuta a kan hanyar Kaura Namoda zuwa Moriki zuwa Shinkafi.

Harbe-harben ya shafi wani tsohon shugaban karamar hukumar Shinkafi, amma ya tsira da raunuka.

Wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Usman, ya ce ya halarci jana’izar Rumba Jengeru a babbar makabartar garin Shinkafi.

Mohammed Usman ya ce sabbin hare-haren da aka kai a Shinkafi da Zurmi da Kaura Namoda da sauran yankuna sun kasance martani ne ga sabbin matakan da gwamnan ya dauka don magance matsalar rashin tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: