Hukumar asusun kiwon lafiya ta jihar Jigawa ta fara aiwatar da shirin kula da lafiyar masu karamin karfi a kyauta

0 92

Hukumar asusun kiwon lafiya ta jihar Jigawa ta fara aiwatar da shirin kula da lafiyar masu karamin karfi a kyauta na gwamnatin tarayya a kananan hukumomi 9 na jihar nan.

Sakataren zartarwa na hukumar Dr Nura Ibrahim ya sanar da hakan ta wani shirin Radio Jigawa.

Yace tuni hukumar ta zabi masu karamin karfi na gwaji su 157 daga kowacce mazaba domin amfana da shirin kula da lafiya a kyauta.

Nura Ibrahim ya kara da cewa ana aiwatar da shirin kula da lafiyar masu karamin karfin ne kyauta a cibiyoyin lafiya 65 kuma an bayar da katin sheda ga wadanda zasu cigajiyar shirin domin samun saukin ganewa.

Nura Ibrahim yace tuni suka aike da kudaden tafikar da shirin ga asibitocin da aka zaba domin aiwatar da shirin.

Yace nan bada jimawa ba za a fadada shirin zuwa sauran kananan hukumomi 21 dake jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: