‘Yan sandan jihar Jigawa sun cafke wasu dalibai 6 bisa tsallaka gidan wani mutum tare da masa aski ta karfi

0 62

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu dalibai 6, bisa zargin su da shiga gidan wani mutum tare da yi masa aski ta karfin tsiya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Lawan Shiisu, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Dutse.

Lawan Shiisu ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 27 ga watan Agusta, bayan wani mutum mai suna Ibrahim Sambo na unguwar Yalwawa da ke Dutse, ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa a ranar 20 ga watan Augusta daliban suka shiga gidansa ba bisa ka’ida ba da misalin karfe 1 na dare, sannan suka aske masa kansa.

Ya ce wanda ya shigar da karar ya yi ikirarin cewa ya yi rashin lafiya kwanaki biyu bayan faruwar lamarin.

Kakakin yansandan ya kara da cewa, bayan samun korafin, jami’an ‘yan sanda sun bazama aiki tare da cafke daliban su 6 wadanda shekarunsa ya kama daga 18 zuwa 19.

Shiisu Adam ya kara da cewa ‘yan sanda sun fara farautar wasu mutane 4 da ake zargi da hannu a lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: