An cafke wani matashi da ya sare hannun wani mutum a Birnin Kudun jihar Jigawa

0 86

‘Yan sanda a jihar Jigawa sun cafke wani matashi dan shekara 20, mai suna Umar Ubale, bisa zargin sa da yanka hannun wani mutum wanda ya kai ga an cire hannun gabadaya.

Mai magana da yawun ‘yan sandan, Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar yau a birnin Dutse kuma ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Zazika da ke karamar hukumar Birnin-Kudu ta jihar.

Lawan Shiisu ya ce an cafke wanda ake zargin ne bayan da ‘yan sanda suka samu rahoto a ranar 22 ga watan Agusta, cewa wanda ake zargin ya sari Hafizu Ya’u dan shekara 30 da adda a hannunsa na dama.

Ya bayyana cewa an garzaya da wanda aka sara zuwa Babban Asibitin Birnin-Kudu domin kula da lafiyarsa, amma sai da aka mayar da shi zuwa asibitin kwararru.

Ya bayyana cewa Umar Ubale da Hafizu Ya’u, mazauna unguwa daya ne, kuma saran da Umar ya yiwa Hafizu yana da zurfin gaske, wanda dole tasa aka yanke hannun gabadaya a Asibitin Murtala dake birnin Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: