‘Yan aware sun sace wani limamin coci a kudu maso yammacin kasar Kamaru

0 56

‘Yan aware sun sace wani limamin coci a kudu maso yammacin kasar Kamaru.

Jami’an cocin sun ce wasu matasa ne suka sace Bishop Julius Agbortoko a ranar Lahadi inda suka nemi kudin fansa.

‘Yan awaren dauke da makamai sun sha garkuwa da mutane, ciki har da shugabannin addinai, tun lokacin da suka soma rikicin neman ballewa daga kasar shekara 4 da suka wuce.

‘Yan awaren na yankin renon Ingila sun jima suna fafutukar neman ‘yancin kansu bayan korafin cewa gwamnati na nuna musu wariya.

Ana zargi dukkanin bangarorin sojin Kamaru da ‘yan aware da aikata laifukan keta hakkin bil adama a lokuta da dama akan fararen hula.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, rikicin da suke ya kai ga mutuwar dubban mutane da tilastawa daruruwa tserewa daga gidajensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: