‘Yan kungiyar ISWAP da na Boko Haram sun kai hari kan wani sansani a jihar Borno

0 76

Mayakan da ake zargin ‘yan kungiyar ISWAP da na Boko Haram ne, sun kai hari kan wani sansani da wasu wurare a garin Rann dake karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.

A cewar PR Nigeria, wata jaridar internet mai alaka ta kut da kut da hukumomin tsaro, mayakan da suka zo da yawa sun samu shiga cikin garin yayin da suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Jaridar ta kuma bayyana cewa mazauna garin, galibin fararen hula sun tsere cikin daji yayin da aka ga ma’aikatan agaji suna tafiya zuwa iyakar kasar Kamaru.

Harin na baya-bayan nan da aka kai garin Rann ya zo ne bayan da wasu mahara suka mika wuya ga gwamnati.

Gwamnatin jihar Borno a kwanan an ta tabbatar da cewa akalla tsaffin mayaka dubu uku wadanda ‘ya’yan kungiyoyin ne sun mika wuya ga sojojin Najeriya.

Gwamna Babagana Zulum ya ce baya ga mayakan da ke hannun gwamnati a yanzu, wasu mayaka 900 da aka tabbatar ‘yan Boko Haram ne, sun mika wuya ga sojojin kasar Kamaru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: