Jihar Nassarawa ta taso keyar Almajirai 788 garuruwansu

0 136

A ƙalla sama da yara masu gararamba a titunan jihar Nassarawa da sunan karatun Allo aka mayar jihohinsu na asali

Gwamnan jihar ta Nassarawa Andullahi Sule ne ya bayyana hakan yayin jawabi ga Almajiran dake jihar da suke cikin rukunin farko da za’a mayar da suka fito daga kudancin jihar.

Ya ce babban dalilin mayar da su shi ne domin su samu cikakkiyar kulawa daga wurin iyayen su ba wai don wani gilli ba.

Almajiran sun haɗar da yan asalin jihohin Jigawa, Plateau, Kaduna, Gombe, da kuma Taraba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: