Jihar Jigawa ta tayi kwangilar kamfani don yiwa Almajiran da aka koro gwajin Korona

0 86

Bayan da jihohin Arewa suka cimma matsaya akan dakatar da al’amarin Almajirci a yankin, ta hanyar mayar da kowanne Almajiri garin da ya fito, yanzu haka jihar Jigawa ta karbi irin wadannan Almajirai da aka koro masu yawan gaske da suka doshi dubu. A hakan ma wasu na kan hanyar su ta zuwa.

Yanzu haka gwamnatin jihar Jigawa ta yi hayar wani kamfani dake Kaduna domin yiwa Almajiran da aka kwaso daga Kano gwajin cutar Korona kafin kyale su shiga cikin gari don komawa cikin iyalansu.

Almajiran da yanzu suke killace a sansanin masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) a ƙaramar Hukumar Kiyawa.

Ƙarin wasu Almajiran 69 da aka debo daga Gombe za’a killace su har tsawon kwanaki goma kafin a gwada su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: