Jiragen Kamfanin Rano Air Zasu Fara Zirga-Zirga A Nigeria

0 95

Hukumar kamfanin sufurin jiragen sama na Rano Air ta ce za ta fara gudanar da zirga-zirgar jiragen a cikin kasa daga ranar Lahadi, 7 ga Mayu, 2023.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a jiya, ya ce gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne zai kaddamar da aikin sufurin jiragen saman kamfanin, a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano.
A kwanakin baya ne dai kamfanin na Rano Air ya bayyana cewa ya kara sayo wasu jiragen sama guda hudu da kudinsu ya kai naira miliyan dubu hudu.
Kamfanin ya kuma ce ya samu takardar shedar yin aiki da jiragen sama daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa wadda ta bawa kamfanin izinin amfani da jiragen sama wajen daukar fasinjoji da kaya da kuma aikin shatar jiragen saman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: