Maniyyata 1,625 Ne Daga Jihar Jigawa Zasu Gudanar Da Aikin Hajjin Bana

0 89

Akalla mahajjata dubu 1 da 625 daga jihar Jigawa da zasu gudanar da aikin hajjin bana sun biya naira biliyan 4 ga hakumar jin dadin Alhazai NAHCON domin aikin hajjin bana.
Babban sakatare na ma’aikatar a jihar jigawa Ahmad Labbo ne ya sanarwa manema labarai cewa hakumar ta tanadar da masaukai masu kyau kusa da Harami ga mahajjatan jihar Jigawa ba kamar sauran shekaru da suka gabata ba.
Ahmad Labbo yace hakumar jin dadin alhazai ta kasa ta zabi kamfanin jiraje na Azman Air domin jigilar alhazai da jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki.
Ya kuma nuna fargaba kan zabar jiragen kamfanin Azman wanda yace suna da iyaka a jihar, yace an shirye-shirye da tsari mai kyau domin tabbatar da aikin hajjin cikin nasara.
A aikin hajjin shekarar data gabata jihar Kano taki amincewa da kamfanin jigila na Azman bisa fargabar rashin isassun kugeru da jinkiri a ayyukansu wajen daukar mahajjata zuwa birnin Makka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: