Gidauniyar Dangote Ta Bada Tallafin N100,000 Ga Wadanda Aka Kwaso Daga Kasar Sudan.

0 114

Gwamnatin tarayya ta yi nasarar kwashe dukkanin ‘yan Najeriya da suka makale a birnin Khartoum na kasar Sudan mai fama da rikici.
Babban sakatare a ma’aikatar jin kai ta tarayya Dr Sani Gwarzo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakoncin kashi na biyu na mutane 130 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Mutanen da aka kwaso sun taso ne daga tashar Alhazai ta filin jirgin saman kasar da misalin karfe 3:10 na rana a cikin Jirgin TARCO daga Port Sudan.
Ya ce an kwaso kashi na biyun mutanen ne ta jirgin sama daga Port Sudan.
Gwarzo ya ce, a cikin mutane 130 da aka kwashe 2 daga cikin su maza ne sauran kuma dukkanin su mata ne, sai yara da kuma marasa lafiya.
Ya kuma bayyana cewa gidauniyar Dangote ta raba wa mutanen tallafin Naira 100,000 kowannen su a matsayin tallafin ceton rai ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: