Ƙaramar Hukumar Hadejia Ta Rusa Shugabancin Kungiyar ‘Yan Kasuwar Masarautar Hadejia

0 101

Karamar hukumar Hadejia ta rusa shugabancin kungiyar ‘yan kasuwar masarautar Hadejia ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan karamar hukumar Alhaji Basiru Ya’u Dunari.
Sanarwar tace rushe shugabancin kungiyyar ya biyo biyan umarnin kotu ne, wadda ta dauki matakin biyo bayan dadewar shugabancin kasuwar ba tare da chanjawa ba.
Sanarwar ta kara da cewa, karamar hukumar ta amince da nada kwamatin mambobi goma (10) a matsayin masu rikon kwarya da za su tafiyar da al’amuran kungiyar kafin zaben sabbin shugabanni.
Wadanda aka nada sun hada da Alhaji Yunusa Shata a matsayin shugaba, Alhaji Ahmed Babangida Sakataren, Hussaini Abdullahi Captain a matsayin jami’in hulda da jama’a.
Sauran sun hada da Alhaji Umar Kaka, Dr Isa Billami, Abdullahi Rambo, Alhaji Sule Tosarawa, Alhaji Ahmed Maidoya, Baffa Garba da Alhaji Maigoro Wakilin ‘Yan Kasuwa a matsayin Membobi.
Wasiƙar ta bayyana cewa tun a ranar 5 ga watan Mayu wannan dokar ta fara an kuma bukaci dukkanin rassan kungiyyar su bi wannan umarnin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: