Jiragen yakin sojojin Najeriya sun yi aman wutar makamai masu linzami akan wasu bikin haure a jihar Katsina

0 128

An kashe ‘yan fashin daji dauke da makamai lokacin da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka yi aman wutar makamai masu linzami akan wani bikin aure da daya daga cikin manyan ‘yan fashin dajin Katsina ya shirya.

Kamar yadda yazo a wani rahoton PRNigeria, wadanda aka kashe sun hada da wani mai suna Sule, wanda shima jigo ne cikin ‘yan fashin daji kuma dan’uwa ne ga wani dan fashin dajin mai suna Lalbi Ginshima.

Sojojin saman sun yi aman wutar ne a kauyen Unguwar Adam dake karamar hukumar Dan Musa ta jihar.

Majijyoyin sirri a Katsina sun sanar da sojojin sama bayanan sirri dake cewa ‘yan fashin dajin sun tashi daga Dan Alikima zuwa Unguwar Adam domin bikin auren daya daga cikin manyan shugabanninsu.

Wata majiya ta gayawa PRNigeria an kashe ‘yan fashin dajin dayawa tare da jikkata wasu da dama, yayin da sauran suka samu raunuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: