

- Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra - May 24, 2022
- Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari - May 24, 2022
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023 - May 24, 2022
‘yan fashin daji sun kashe mutane dayawa cikin har da ‘yansanda a garin Ngaski da kauyen Gafara dake karamar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi.
Da yake tabbatar da harin ga sashen Hausa na Muryar Amurka, dan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar Yawuri, Shanga, Ngaski, Yusuf Tanko Sununu, yace ‘yan fashin dajin sun aika da wasika dake cewa zasu kawo hari kauyen inda wani kamfanin sarrafa tumatir yake.
Yace bayan sun aika da wasikar, hukumomin kamfanin sun kwashe ‘yan kasar China da sauran ma’aikatan dake aiki a kamfanin kuma aka sanar da jami’an tsaro amma duk da haka ‘yan fashin dajin suka kaddamar da harin a jiya da rana.
Dan majalisar yace an samu gawarwaki biyu amma ya nemi wakilin VOA Hausa ya jira domin karin bayani nan gaba.
Sai dai, wani da ya shaida lamarin ya gayawa manema labarai cewa yawan mutanen da aka kashe yana karuwa amma akalla ‘yansanda 10 aka kashe.
Kakakin ‘yansanda na jihar Kebbi, Nafi’u Abubakar, bai amsa kiran wayarsa ba domin martani dangane da harin.