Kananan yansanda ne ke shirin tafiya yajin aiki ba mu ba – Yansanda

0 95

Akasi bisa ikirarin da hukumomin ‘yansanda suka yin a karyata labarai dangane da yajin aikin da kakanan ‘yansanda ke shirin tafiya, wata takarda da aka bawa manema labarai ta nuna cewa da gaske kananan ‘yansanda suna shirin tafiya yajin aiki.

Takardar wacce tazo cikin wani sakon ‘yansanda da jaridar Premium Times ta gani, ta yi nuni da cewa kananan ‘yansandan zasu tafi yajin aikin ne saboda kasa fara aiwatar da sabon tsarin albashin ‘yansanda da kuma kin samar da makaman yaki masu kyau wajen yakar bata gari tare da rashin kulawa da walwalar ‘yansanda.

Takardar tace tuni sufeto janar na ‘yansanda ya bayar da umarnin gaggauta lissafa albashin a karkashin sabon tsarin albashin tare da hutun biyan haraji ga ‘yan sanda ko cire su daga cikin masu biyan harajin, domin gaggauta aiwatarwa.

Ta kuma kara da cewa helkwatar ‘yasanda ta fara da kammala rabon kaki da sauran kayayyakin aiki.

Hukumomin ‘yansanda shekaranjiya Litinin sun kayi kokarin karyata labaran dake cewa ‘yansanda na shirin tafiya yajin, inda suka bayyana rahotannin da na bogi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: