Juyin Mulkin Sojoji Ya Rutsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Kasar Guinea Bissau

0 338

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea Bissau, lamarin da ya kai ga tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da sauran ⁠masu sa ido na ƙasashen waje makale a ƙasar.

Jonathan ya je a matsayin jagoran dattawan Afrika (West African Elders Forum – WAEF) don sa ido kan zaben da ake gudanarwa, amma bayan da sojoji suka ayyana karɓar mulki, suka rufe iyaka, suka sa dokar tafiyar dare, kuma suka dakatar da zaben, Jonathan da sauran bakin da suka je kasar ba za su iya fita ba.

Sojojin sun kama wasu manyan jami’an kasar da Guinea Bissau, ciki har da shugaban adawa, sannan sun ce sun hambarar da Shugaba Umaro Sissoco Embaló.

Jonathan da sauran shugabannin Afrika da ke cikin ƙasar sun fitar da sanarwa, suna Allah-wadai da juyin mulkin, tare da kira ga AU da ECOWAS su dawo da tsarin mulkin Dimokradiyya.

Duk da kasancewarsa makale, rahotanni sun tabbatar cewa Jonathan yana cikin koshin lafiya.

Leave a Reply