Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsira Bayan Ayarinsa Sunsamu Mummunan Hatsari a Hanyar Maigatari

0 686

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, ya tsallake rijiya da baya, bayan da ayarinsa suka yi mummunan hatsari a kan hanyar zuwa karamar hukumar Maigatari jiya Litinin a jihar.

Kamar yadda jaridar ‘Newspoint Nigeria’ ta ruwaito, Shugaban Majalisar na kan hanyar zuwa Maigatari ne domin halartar wani gangamin siyasa da aka shirya a karkashin wani shiri mai taken “Dandalin tattaunawar Gwamnati da Jama’a” a lokacin da lamarin ya afku.

Wani wanda lamarin ya afku a gabanshi, ya bayyana cewa ayarin motocin na kan hanyar zuwa wurin taron ne sai daya daga cikin motocin da ke bayar da kariya ga shugaban, wata mota kirar Toyota Hilux ɗauke da jami’an ‘yansanda ta ƙwace, sannan ta yi ta hantsalawa.

 Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.

 Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.

Leave a Reply