Kamfanin 9mobile ya rasa kwastomomi 6,079 a watanni biyu kacal

0 70

Kamfanin sadarwa na 9mobile na ci gaba da rasa kwastomomi, inda mutane 6,079 suka koma wasu kamfanoni a watanni biyu kacal.

Rahoton Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC) ya nuna cewa a watan Disambar 2024 kadai, mutum 2,188 ne suka bar 9mobile.

A cikin Nuwamba, mutum 3,891 ne suka fice daga kamfanin, wanda hakan ke nuna raguwar kaso mai yawa daga masu amfani da layukansa.

A halin yanzu, 9mobile na da kaso 1.9% na kasuwar sadarwa a Najeriya, sabanin matsayinsa a shekarun baya da ya kai kaso 15.7% a shekarar 2015.  

Leave a Reply