Kamfanin KEDCO zai ci gaba da gudanar da shirin raba mitoci a gidaje kyauta

0 103

Kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO tace, yanzu hakan tana cigaba da gudanar da shirin nan na raba mitoci a gidaje, ta kuma bukaci duk wanda baisamu mitar ba, zai iya tura bukatar neman mitar cikin gaggawa domin samun ta.

Ta kuma kara da cewa mutum zai iya neman mitar daga bisani a cire kudinta ta hanyar wutar da yake sha, na tsawon shekaru 3.

Ko kuma mutum ya sayi mitan mai dauke da layin wuta daya wato one phase akan naira dubu 36,000.

Sai kuma mai dauke layukan wuta uku wato three phase akan naira dubu 117,00

A cewar KEDCO duk mai bukata zai iya zuwa ofishin kamfanin mafi kusa da shi domin bayyana bukatar sa.

Kamfanin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya aikewa gidan radio sawaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: