Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya su tsammaci cigaba a shekarar 2022, biyo bayan tarin kalubalan da suka dabai baye kasar nan ta fuskar cigaban tattalin arziki.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a sakon sa na sabuwar shekarar 2022, wanda ya aikewa yan Najeriya.

Haka kuma ya bukaci yan Najeriya su manta da bambamce-bambamcen addini da Siyasa don hada hannu wuri guda domin hada kan kasar nan tare da yakar matsalolin da kasar nan take ciki.

A cewarsa, matsalolin da suke damun kasar nan musamman ta fuskar tsaro abu ne da ya ke kawowa gwamnatin sa koma baya, wajen ciyar da kasar nan gaba.

Kazalika, ya bawa yan kasar nan tabbacin cewa gwamnatinsa zata yi duk mai yuwuwa domin bijiro da shirye-shiryen da zasu kyautata rayuwar yan kasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: