Hukumar kula da tsaftar mahalli ta jihar Jigawa ta kaddamar da aikin tsaftace tashoshin mota da wuraren wanka da bahaya

0 104

Hukumar kula da tsaftar mahalli ta jihar Jigawa ta kaddamar da aikin tsaftace tashoshin mota da wuraren wanka da bahaya a wasu kananan hukumomin jihar nan tara.


Manajan Daraktan Hukumar Injiniya Lawan Ahmed Zoma ya kaddamar da aikin na kwanaki tara a tashar motar dake Dutse.


Yace aikin na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar da kuma hukumar samar da ruwan sha da tsaftar mahalli a yankunan karkara da nufin hana alumma yin bahaya a waje.


Injiniya Lawan Ahmed Zoma ya shawarci yan kungiyar direbobi da yan kasuwa da sauran kungiyoyi masu zaman kansu su marawa gwamnati baya wajen hana bahaya a bainar jama-a da kuma kula da tsaftar mahalli.


A jawabin sa Daraktan kula da tsaftar mahalli na hukumar Alhaji Adamu Sabo ya bada tabbacin samarda isassun kayayyakin aiki domin samun nasarar aikin.


Ya kuma yabawa hukumomin biyu bisa kokarin su na kare lafiyar alummar jihar nan daga kamuwa da cututtuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: