Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa zata kammala aikin kwaltar jirgin kasa daga Kano zuwa Kaduna kafin karshen 2022

0 103

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa zata kammala aikin kwaltar jirgin kasa daga Kano zuwa Kaduna kafin karshen 2022.

Ministan sufirin jiragen kasa Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan, a lokacin dayake duba yanda aikin yake gudana a birnin Kano.

A cewar sa za’abude wannan aikin ne kafin shugaban kasa Muhammadu buhari ya sauka a karshen 2023.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayya ta zuba kimanin Dollar biliyan 400 domin gudanar da wannan aikin.

Rotimi Amaechi ya kuma bukaci kamfanin dake gudanar da wannan aikin, ya kara yawan kayan aiki da ma’aikata domin samun nasarar kammala aikin akan lokaci.

Kafin kafin hakan an shirya shimfida hanyar layin dogon ne mau dauke da tashoshi 15, wacca zata tashi daga Kano-Dambatta-Kazaure-Daura-Mashi-katsina-Jibiya sannan ta dire a garin Maradi dake jamhuriyyar Nijar.

Zata kuma shiga kauyuka da birane da dama idan akak kammala wannan aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: