Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Karɓi Buƙatar Gwamnatin Jihar Na Neman Amincewar Majalisar Domin Karɓar Bashin Naira Biliyan 84

0 97

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta karɓi buƙatar Gwamnatin Jihar na neman amincewar majalisar domin karɓar bashin naira biliyan 84 a zaman da aka gudanar ranar Talata.

Zaman majalisar ya gudana ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Haruna Aliyu Dangyatin, bayan buɗe zama da addu’a kamar yadda doka ta tanada.

Takardar da ta fito daga gidan gwamnatin jihar ta bayyana cewa bashin na daga cikin tsarin tallafin kuɗi da Gwamnatin Tarayya ta tanada wa jihohi, inda kowacce jiha za ta iya karɓar rance ta hannun bankin da ke hulɗa da ita.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ce za ta riƙa biyan kuɗin bashin kai tsaye ta hanyar cire kusan naira biliyan bakwai duk wata na tsawon shekara guda, ba tare da gwamnatin jihar ta biya daga asusunta kai tsaye ba.

Leave a Reply