Gwamnatin Jigawa Da UNICEF Za Su Horar Da ’Yan Mata 1,500 Sana’o’in Dogaro Da Kai

0 88

Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar UNICEF za su ɗauki nauyin ’yan mata 1,500 domin koyar da su ilimin manya da kuma sana’o’in dogaro da kai a faɗin jihar.

Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata ta jihar, Hadiza AbdulWahab, ta bayyana hakan bayan rangadin duba wasu cibiyoyin horaswa da ke ƙananan hukumomin Dutse da Kiyawa.

Ta bakin Daraktar lura da al’amurran ƙananan yara, Halima Yusuf Usman, an bayyana cewa za a fara gudanar da shirin ne a matsayin gwaji a ƙananan hukumomin Birnin Kudu da Dutse da Jahun da kuma Kiyawa.

Rahotanni sun ce an zaɓo mata 25 daga kowacce mazaɓa a ƙananan hukumomin guda huɗu domin cin gajiyar shirin, wanda zai fi mayar da hankali kan ’yan mata masu shekaru tsakanin takwas zuwa 14 waɗanda ba sa zuwa makaranta.

Haka kuma, gwamnatin ta ce dole ne kowacce yarinya da za ta shiga cikin shirin ta samu amincewar iyayenta kafin fara horaswar.

An bayyana cewa za a gudanar da horaswar na tsawon makonni takwas, sannan daga bisani a bai wa waɗanda suka halarta kayan sana’o’in dogaro da kai domin fara sana’a.

Wasu daga cikin iyayen yaran sun yabawa gwamnatin jihar da UNICEF bisa wannan shiri da suka ce zai taimaka wajen inganta rayuwar ’ya’yansu.

Leave a Reply