Hukumar lura da manyan makarantun sakandare ta Jihar Jigawa ta gudanar da bikin buɗe tayin bayar da kwangilar sayen ƙarin motocin aiki da kayayyakin fasahar sadarwa na zamani (ICT).
Da yake jawabi a wajen bikin da aka gudanar a babban ɗakin taro na hukumar, shugaban hukumar, Abubakar Sabo Yushau, ya bayyana cewa kayayyakin da za a sayo sun haɗa da motocin aiki guda takwas da ƙananan kwamfutoci guda 30 da injinan buga takardu guda 50 da kuma manyan kwamfutocin tebur guda 100.
Ya ce sayen sabbin motocin zai taimaka wajen inganta ayyukan hukumar tare da magance matsalolin sufuri da ake fuskanta.
Farfesa Abubakar Sabo Yushau ya ƙara da cewa wannan na daga cikin manufofin gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Umar Namadi na bunƙasa harkokin ilimi a jihar.
Shugaban hukumar ya kuma tabbatar da cewa an bi dukkan ƙa’idoji da sharuddan gudanar da tayin kwangila kamar yadda doka ta tanada.
A jawabansu daban-daban, wakilan hukumar tantance bayar da ayyukan kwangila da ma’aikatar shari’a da ofishin mai binciken kuɗi na jihar da kuma ƙungiyoyin yaƙi da cin hanci sun yabawa hukumar bisa yadda ta gudanar da tsarin cikin gaskiya da adalci.