Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Kamaye, An Rasa Rayuka Da Jikkata Wasu

0 63

Wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Ƴan Kamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa, jihar Kano; inda suka buɗe wa mutane wuta ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

Rahotanni sun ce harin ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu mutane, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban sakamakon harbin bindigar.

Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin firgici, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kai ɗauki ga waɗanda suka jikkata. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba.

Leave a Reply