Jami’an tsaro na jihar Zamfara sun samu nasarar kubutar da mutane 10 bayan anyi garkuwa da su

0 103

Gamayyar jamian tsaro dake aiki a jihar Zamfara sun samu nasarar kubutar da mutane 10 bayan anyi Garkuwa da su.

Kafin hakan dai anyi Garkuwa da mutanen ne a garin Gada dake yankin Karamar hukumar Bungudu dake jihar.

Bayan yan bindigar sun farwa garin da misalin karfe 3 na rana tare da kashe Mai garin Ummaru Bawan-Allah.

A cewar kwamishinan yasandan jihar Ayuba Elkanah a lokacin dayake zantawa da manema labarai a Gusau babban birinin jihar, ya tabbatar da kashe mai gari tare da wasu mutane 4.

Ya kuma kara da cewa wadanda aka kubutar tin, tina kaa hada su da yan’uwansu, cikin su harda wani wani jariri dan shekara 1 da aka sace tare da mamarsa.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa, sun samu nasarar kama wasu kasurguman yan fashin daji dake addabar iyakokin Zurmi da Shinkafi dake jihar zamfaran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: