Kamfanin Max Air zai fara jigilar maniyatan Jigawa zuwa Saudiya a ranar 20,21 ga watan Mayu 2025

0 125

Kamfanin jiragen sama na max air ya ce zai fara jigilar maniyatan jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 da kuma 21 ga watan Mayu 2025.

Daya daga cikin jagororin kamfanin Mr Barnabas Adanson ne ya tabbatar da hakan a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan aikin hajji da hukumar jin dadin alhazai ta jiha ta gudanar a babban dakin taro na hukumar

Ya ce jirgin max air zai yi sawun farko da maniyatan Jigawa 550 zuwa Birnin Jeddah ranar 20 ga wata sannan kuma jirgi na biyu zai dauki maniyatan Jigawa 400 zuwa Jeddah a ranar 21 ga wata

Mr Barnabas ya kara da cewar jami’an kamfanin zasu iso Dutse a ranar 19 ga wata domin kammala duk wani shiri na jigilar maniyatan zuwa kasa mai tsarki

Ya tabbatarwa da masu ruwa da tsaki cewar kamfanin max air zai tabbatar da ganin an yi jigilar maniyatan cikin lumana da kuma kwanciyar hankali

A jawabinsa wakilin hukumar aikin hajji ta kasa mai kula da jihohin Kano da Jigawa Salisu A. Gaya ya ce hukumar zata tabbatar da ganin an yi jigilar maniyatan cikin tsari.

Ya kuma bukaci maniyata dasu kiyaye da kai’doji da kuma dokokin kasa mai tsarki domin kare kima da kuma martabar jihar jigawa da ma Nigeria baki daya.

Leave a Reply