Kamfanin wasanni na Britaniya ya zo neman ƴan ƙwallon ƙafa a Jihar Kano

0 164

Kamfanin wasanni na Britaniya ya zo neman ƴan ƙwallon ƙafa a Jihar Kano
Wani kamfanin wasanni na Britaniya, Anchor Sports ya iso Jihar Kano domin ɗiban ƴan wasa masu hazaka.A wata sanarwar da Daraktan kamfanin a Nijeriya, Abdulgaffar Oladimeji ya fitar, kamfanin ya zo ne domin zaɓo matasa ƴan ƙwallon ƙafa ya kai su ƙasar Switzerland.


Oladimeji ya ce za a yi gwajin ƴan wasan a ranakun 12 da 13 ga watan Maris a filin wasa na Jami’ar Bayero Kano, BUK, inda ya ƙara da cewa matasa ƴan shekara 17 zuwa 21 kawai za a gaiyata.Ya ce kamfanin ya zaɓi Kano ne sabo da ƙaunar matasan Kano ga wasanni, musamman ƙwallon ƙafa, inda ya ƙara da cewa jihar na da albarkar ƴan ƙwallon ƙafa masu hazaka.Oladimeji ya ce za a fara tantance ‘yanwasan da misalin karfe 8:00 na safe.


A ko wacce jihar a ke, in ji Daraktan, za a iya kiran wadannan lambobi:Muzammil Dalha Yola 08057272222.Anunobi 09069977344.Abdulgaffar Oladimeji 07033671325.


Ana gayyatar dukkanin wanda ya ke buga kwallo ko kuma kungiyarsa domin shiga wannan tantancewa.

-DailyNigerian

Leave a Reply

%d bloggers like this: