An bayar da umarnin kwashe dukkan motocin da aka kama da kuma kayayyakin da ba a yi wa rajista ba daga ofisoshin ‘yan sanda

0 24

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin kwashe dukkan motocin da aka kama da kuma kayayyakin da ba a yi wa rajista ba daga ofisoshin ‘yan sanda a fadin kasar nan.

Mukaddashin Jami’in hulda da Jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Adejobi ya ce, umarnin ya biyo bayan tsarin yadda aka jibge motocin a ofisoshin ‘yan sanda.

A cewarsa, babban sufeton ‘yan sandan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake tara motocin da aka kwato daga wuraren da ake aikata laifuka ko kuma wadanda ake tababa kan mamallakansu.

Ya ce lamarin ya kara dagulewa ta hanyar tsauraran sharudda da kuma tsauraran matakai ga masu motocin wajen karbarsu.

Kakakin ya ce, Sufeto-Janar na ‘yan sandan ya umurci shugabannin ofisoshin ‘yan sanda da su fara bin tsarin da ya dace don gudanar da tantancewa da kuma mika motocin ga masu su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: