Labarai

Kungiyar Jama’atul Nasril Islam ta kasa ta bada shawarar kafa dokar karba da kuma rabon Zakka a tsakanin alummar musulmai

Kungiyar Jama’atul Nasril Islam ta kasa ta bada shawarar kafa dokar karba da kuma rabon Zakka a tsakanin alummar musulmai.

Hakan na kunshe ne a cikin takardar bayan taron da kungiyar da ta gudanar kan tsarin zamantakewa da tsaro a Mahangar Addini a Dutse babban birnin Jihar Jigawa.

Takardar bayan taron mai dauke da sa hannun sakatare Janar na kungiyar na kasa Dr. Khalid Abubakar Aliyu da kuma shugaban kwamitin daftarin bayan taro Alhaji Abdulkadir Abubakar Maje sun bukaci jihohi dasu dauki kwararan matakai na dakile rashin ilmi da fatara da talauci da rashin aiyukan yi a Jihohinsu.

Haka kuma takardar bayan taro ta bukaci masu hali dasu rinka bayar da zakka da kafa kwamitin zakka da waqafi karkashin mai alfarma sarkin musulmi da kuma kafa kwamiti da zai wayar da kai alumma kan muhimmanci zakka da kuma waqafi.

Kungiyar Jama’atul Nasril Islam ta yabawa gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa daukar nauyin babban taron a Dutse.

Malama addini sun gabatar da kasidu daban-daban a lokacin taron.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: