Kamfanonin jirage da dama sun ɗauki matakin kauracewa sararin samaniyar Iran

0 106

Kamfanonin jirage da dama sun ɗauki matakin kauracewa sararin samaniyar Iran, a daidai lokacin da rikici ke kara kamari a yankin.

Jirgin Qantas na Australia da Lufthansa na Jamus na karkata akalarsu ta bin hanyoyi masu nisa, yayin da aka dakatar da dukkan jirage daga ƙasashen yamma zuwa Iran inda suka bi sauran takwarorinsu da suka kaucewa bin ƙasar.

A ranar Juma’a shugaba Joe Biden na Amurka, ya ce ya yi amanna babu abin da zai hana Iran mayar wa Isra’ila kakkausan martani, amma duk da hakan ya yi kakkausan gargaɗi ga ƙasar kada ta kuskura ta aikata hakan. Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Amurka sun girke kayan aiki a Isra’ila domin ba ta kariya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: