Karamar Hukumar Kazaure ta biya miliyan 2.4 domin tallafawa daliban yankin dake karatu a jami’ar SLU
Karamar Hukumar Kazaure ta ce ta kashe kudi naira miliyan biyu da dubu dari hudu da arbain wajen biyan tallafin karatu ga daliban yankin dake karatu a Jami-ar Sule Lamido Kafin Hausa
Shugaban KH Alhaji Mansur Usman Dabuwa ya sanar da hakan a lokacin rabon tallafin karatun a harabar Jamiar
Ya kara da cewar kusan dalibai 204 ne suka ci gajiyar shirin a wani mataki na bunkasa harkokin karatu
Alhaji Mansur Usman Dabuwa ya kuma ce KH ta kashe kudi naira miliyan daya da rabi wajen samar da littattafan rubutu da alli da sauran kayayyakin koyo da koyarwa a makarantun firamare da kuma kananan makarantun sikandaren yankin
A jawabinsa Darakta maaikata na yankin Alhaji Shu’aibu Naa’abo ya bukaci daliban da su maida hankali wajen yin karatu
Shima da yake jawabi sakataren harkokin malamai na jamiar Malam Izaddin Ibrahim Dan Malikin Taura ya yabawa shugaban KH bisa wannan karamci wanda hakan zai karawa dalibai kwarin gwiwa wajen yin karatu
Shima shugaban kungiyar dalibai na jamiar Sule Lamido Comrade Adamu Musa ya yaba da kokarin gwamnatin jiha na bunkasa harkokin ilmi