Kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar jigawa tga zabi sabbin shugabanni a karo na 8 da zasu ja ragamar harkokin kungiyar.
An zabi Ismaila Ibrahim Dutse a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridun ba tare da hamayya ba a taron wanda aka gudanar da sakatariyar kungiyar da ke Dutse.
Da ya ke sanar da sakamakon zaben, mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyya ta daya, Tukur Umar Muhammad ya ce haka kuma an zabi Nura Sani Bello da Najib Umar da Aminu Umar Shuwajo ba tare da hamayya ba yayin da Aisha Ahmad ta kamfanin dillancin labarai na kasa NAN da ke Dutse ta samun nasara da yawan kuri’u 45 inda ta zamo sakatariyar kungiyar, sai kuma Auwal Muhammad Kazaure wanda ya samu nasara da yawan kuri’u 69 inda ya zamo ma’ajin kungiyar.
Sakataren kungiyar na shiyya, Abdulrazak Bello Kaura ne ya rantsar da sabbin shugabannin.
A jawabinsa, sabon shugaban kungiyar NUJ Ismaila Ibrahim Dutse ya bayyana zaben sa ba tare da hamayya ba a matsayin wani babban karimci da aka nuna masa, inda ya godewa masu ruwa da tsaki ciki har da Gwamna Umar Namadi bisa gudummawar da su ka bayar wajen samun nasarar zaben.