Karamar Hukumar Taura ta bada wa’adin kwanaki 7 ga Mata masu zaman kansu da gidajen Giya

0 233

Majalisar Karamar Hukumar Taura ta nan Jihar Jigawa ta bada wa’adin kwanaki 7 ga Mata Masu zaman kansu da kuma masu gidajen Giya su bar karamar hukumar cikin gaggawa.

Shugaban Majalisar Karamar hukumar Alhaji Baffa Yahaya, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake jagorantar zaman Kwamatin Tsaro na Karamar hukumar.

A cewarsa, hakan zai tallafawa kokarin karamar hukumar na ganin cewa ta inganta tsaro a yankin.

Shugaban ya ce Majalisar ta haramta Karuwanci da Shan giya, fadin karamar hukumar Taura, inda ya kara da cewa duk wanda aka kama zai fuskanci fushin Shari’a.

Haka kuma Shugaban ya ce an bawa Masu Sana’ar wa’adin kwanaki 7 su sauya sana’a ko kuma su bar fadin karamar hukumar.

Alhaji Baffa Yahaya, ya ce Majalisar zata dauki matakin doka kan duk mutumin da ya karya dokar da ta shinfida.

Wannan na zuwa ne bayan da Majalisar karamar hukumar Gwaram ta shimfida, irin wannan dokar ga Mata Masu zaman Kansu da kuma Masu Gidajen Giya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: