An kwaci mata 19 yayin safarar su zuwa Nahiyar Turai a Jihar Jigawa

0 76

Hukumar Hana Safarar Mutane, ta Kasa NAPTIP ta ce tayi nasarar kubutar da wasu yan Mata 19 tare da kama mutane 4 da take zargi da fataucin mutane a nan Jihar Jigawa.

Shugaban Hukumar na Kasa Sanata Basheer Garba Muhammad, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano, inda ya ce wadanda aka ceto mata ne wadanda shekarunsu ya kama daga 14 zuwa 29, kuma ana kokarin safarar su ne zuwa Nahiyar Turai.

A cewarsa, hukumar ta sami rahoton Sirri cewa wadanda ake zargin sun boye wadanda za ayi safararsu a nan jihar Jigawa, kafin daga bisani a tafi dasu a rukuni-rukuni zuwa jamhuriyar Nijar.

Haka kuma ya ce bayan samun rahoton ne hukumar tayi hadin gwiwa da rundunar yan sandan Jihar Katsina inda ta ceto Yan Mata 19.

Kazalika, ya ce sun kuma kama mutane 4 bisa zargin su da safarar Mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: