Rundunar yan sandan jihar Kano ta gano maboyar barayin shanu guda 2 tare da kama mutum 10

0 96

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta gano Maboyar Barayin Shanu guda 2, tare da kama mutane 10 bisa zargin su da aikata  laifukan.

Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.

A cewarsa, an kama mutanen ne biyo bayan rahoton da rundunar ta samu kan fashin da akayi a kananan hukumomin Ajingi da Tudun Wada.

Haka kuma ya ce rundunar ta samu rahoton wasu batagari sun sace shanu 2 a kyauyen Kara da Dagaji na karamar hukumar Ajingi ta jihar.

DSP Kiyawa, ya ce bayan samun rahoton rundunar ta garzaya wurin, inda tayi nasarar kama barayin, tare da kubutar da Shanu 5.

Mutanen da ake zargin sun hada da Usman, Ado Dare, Amadu, Ibrahim Dare, Mohammed, Musa, Isa and Muhammad.

Sannan rundunar ta kama Sama’ila Adamu da Aliyu Muhammad bisa zargin su da hada baki wajen sace Shanu a kyauyen Jandutse na karamar hukumar Tudun Wada.

Kazalika, ya ce za’a gabatar da mutanen a gaban Kotu bayan kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: