Hukumar NYSC reshen jihar Kaduna ta ce matasa 19 da suka harbu da cutar Corona sun warke

0 90

Hukumar Matasa Masu yiwa Kasa Hidima ta NYSC reshen Jihar Kaduna ta ce Matasa 19 da aka tura Jihar wanda suka harbu da cutar Corona sun warke kuma tuni aka sallame su.

Shugaban Ofishin Hukumar na Jihar Kaduna Malam Isah Wana, shine ya bayyana hakan a jiya a lokacin da ya karbar Faretin girmamawa daga wurin Matasan yan rukunin B, na (I) su dubu 1,500 da suka samu horo a Sansanin horas da Matasan na Jihar Kaduna.

A nasa Jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-rufa’i ya yi alkawarin samar da tsaro ga Matasa da aka turo Jihar.

Gwamnan, wanda Kwamishiniyar Ma’aikatar Jindadi da Walwalar Jama’a Hafsat Baba ta wakilta, ya ce gwamnatin zata samar da tsaro ga Matasan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: