A kalla mutum 7 ne suka mutu, yayin da kuma aka kwantar da wasu saboda cutar kwalara a jihar Taraba

0 58

A kalla mutane 7 ne suka mutu, yayin da kuma aka kwantar da wasu da dama a Asibiti, biyo bayan barkewar cutar Kwalara a garin Tella na karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba.

Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya na Jihar ta Taraba Dr Innocent Vakkai, shine ya tabbatar da hakan ga gidan Talabijin na Channels Tv ta wayar tarho.

A cewarsa, an tura tawagar kwararru daga Ma’aikatar Lafiya domin bincikar faruwar lamarin tare da mika rahoton sa.

Haka kuma ya ce rahoton da aka gabatarwa Shugabar Karamar Hukumar ta Gassol Musa Chul, ya yi nuni da cewa kimanin mutane 25 ne aka kwantar dasu a Asibitin garin Tella.

Kwamishinan, ya ce wurin da cutar tafi tsanani shine Unguwar Kabawa, wanda yake makotaka da garin Tella.

Shugaban Karamar Hukumar ya shawarci mazauna yankin su rika tsaftace muhallansu domin dakile yaduwar cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: