Yansanda sun kama wasu gungun yan fashin da makami da suke addabar karamar hukumar Ringim

0 80

Rundunar yansandan jihar jigawa ta kama wasu gungun yan fashin da makami da suke addabar karamar hukumar Ringim da makotanta.

Karamar hukumar Ringim tayi kaurin suna wajan dawwamamman zaman lafiya da ake samu shekaru da dama da suka gabata, amma a yan shekarun nan bata gari sun warzaga zaman lafiyan da ake samu a karamar hukumar.

Hakanne yasa majalissar karamar hukumar ta sanya dokar hana babura masu kafa 2 aiki daga 12 na dare, domin samun damar kama barayi a karamar hukumar.

Kakakin rundunar yansandan jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da kama yan fashin su 2, bayan wasu manyan sumame da kaiwa barayin.

Ya kara da cewa yayin gudanar da binciken su, baraynin sun tabbatar da cewa sune wadanda suke addabar Ringim da makwabtanta.

Haka kuma ya jaddada cewa sun kammala shiryawa domin kamo sauran mambobbin kungiyyar.

Ya kuma bukaci mutanen dake karamar hukumar ta Ringim da su basu hadin kai idan sukazo neman bayanai a wurinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: