Gwamnatin tarayya ta bukaci yan Najeriya da kada su dauki Makami a hannayen su

0 104

Gwamnatin tarayya ta bukaci yan Najeriya da kada su dauki Makami a hannayen su domin kare kansu daga hare-haren yan bindiga ba bisa ka’ida ba.

Ministan Ma’aikatar Kula da Ayyukan Yan Sanda Malam Muhammed Dingyadi, shine ya bayyana hakan a jiya, a lokacin da yake yiwa Manema Labarai Jawabi a Ofishin yanSanda dake Abuja.

Ministan ya bayyana hakan ne, biyo bayan kalaman da wasu manyan mutane sukeyi, na su fito su kare kansu daga hare-haren yan bindiga da masu Garkuwa da mutane.

Matsalar tsaro na cigaba da kawo cikas a Najeriya musamman Arewacin Kasar, wuraren da yan bindiga da barayin shanu suke cigaba da kaiwa hare hare.

A makon da ya gabata ne Gwamna Aminu Bello Masari ya bukaci mazauna Jihar Katsina su fito su kare kansu daga matsalar tsaron dake cigaba da addabar yankin.

Amma da yake jawabi ga manema Labarai Mista Dingyadi, ya ce gwamnan yana da damar ya fadi albarkacin bakin sa.

Kazalika, Ministan ya amince da cewa Najeriya na fuskantar matsalar tsaro, sai dai ya ce kowanne dan Najeriya yana da rawar da zai iya takawa domin kubutar da yankin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: