Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci a sake fasalin tsaron Najeriya tare da tsige Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara a fannin tsaro

0 170

Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci a sake fasalin tsaron kasar nan, tare da tsige Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara a fannin Tsaro Major General Babagana Monguno Mai Ritaya, biyo bayan harin da aka kaiwa Kwalegin Horas da Hafsoshin Tsaro.

Kungiyar ta bayyana harin da yan bindiga suka kai makarantar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Sojoji 2, tare da sace Mutum 1, a matsayin kwacewar fasahar mai bawa kasa shawara akan tsaron.

Tun da farko, hukumar Makarantar, ta tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kashe Manyan Sojoji 2 a makarantar wanda take Afaka ta Jihar Kaduna.

Kungiyar ta Dattawan Arewa cikin wata sanarwa da Jami’in ta na Kasa Engineer Zanna Goni, ya fitar biyo bayan kaiwa harin,

Ya ce hakan yana nuni da cewa dole a sake yiwa fasalin tsaron kasar nan garanbawul, tare da zargin Sakacin hafsoshin tsaro.

Kazalika yace, kungiyar ta nuna alhininta kan harin tare da bayyana cewa Babagana Monguno, bai cancanci tsayawa a mukamin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: