Kasar Kamaru ta tilasta wa ma’aikatan gwamnati su ringa halartar wasannin gasar cin kofin kasashen Afirka

0 88

Hukumar kula da ma’aikata a garin Buea da ke yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru ta tilasta wa ma’aikatan gwamnati su ringa halartar wasannin gasar cin kofin kasashen Afirka.

Hakan dai ya biyo bayan umarnin da gwamnan yankin ya bayar, kamar yadda magajin garin ya nuna cewa halartar filin wasan wajibi ne ga kowa.

Matakin ya zo ne bayan an buga wasanni da dama a garin Limbe inda mutane kadan ne suka shiga filin wasan.

Mazauna yankin na Buea da dama na fargabar samun arangama tsakanin ‘yan aware da sojoji.

‘Yan awaren wadanda suka kaddamar da yaki da gwamnati shekaru biyar da suka gabata sun yi barazanar kawo tsaiko a wasannin, amma gwamnati ta tabbatar da samar da tsaro.

Birane da dama sun samar da motocin bas-bas da kananan motoci don ba wa mutane da yawa damar halartar wasannin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: